in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika 3 zasu yaki laifukan farautar giwa
2016-04-30 13:07:39 cri

Shugabannin kasashen Kenya da Uganda da Gabon sun kira taron koli a jiya Jumma'a a kasar Kenya, domin tattaunawa kan yadda za a kare giwaye da sauran namun daji wadanda ba su da yawa a Afrika, kana sun yi niyyar hada kai wajen yaki da laifuffukan farautar giwaye da cinikin hauren giwayen ba bisa ka'ida ba.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya bayyana a gun taron cewa, yadda dan Adam ke ayyukan farauta da kuma lalata muhallin hallitu da kuma sauyawar yanayi sun yi sanadiyyar raguwar yawan giwaye, hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban wani muhimmin mataki ne wajen yaki da irin wadannan laifuka yadda ya kamata.

Sannan yayi kira ga kasashe daban daban da su dauki matakai masu amfani wajen kare giwa da kuma sauran namun daji wadanda ba su da yawa a Afrika.

Bisa kididdigar da aka bayar a gun taron kolin, yawan giwayen Afrika ya ragu da kashi 62 cikin dari tun daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2011, kana tun daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2012 an kashe giwaye dubu 100 ta hanyar farautarsu.

Ban da haka kuma, shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni ya bayyana cewa, dole ne a maida hankali kan kasuwar sai da kayayyakin namun daji domin kare giwaye da yaki da laifukan farautarsu. Kuma ya kamata a yi kokarin yaki da cin hanci da kawar da talauci wadanda ke haddasa laifukan farautar namun daji.

A nasa bangaren, shugaban kasar Gabon Omar Bongo ya yi kira ga kasashe daban daban da su yi koyi da juna kan ilmin yaki da farauta, ya jaddada cewa, ya kamata a kawar da sabanin dake karuwa a tsakanin namun daji da bil Adam.

Kazalika, wasu wakilan kungiyoyin kare namun daji da wakilin musamman na shugaban kasar Amurka da jakadun kasashen Sin da Rasha dake kasar Kenya sun halarci wannan taro.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China