in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farautar giwaye ta dan ragu ko da yake da sauran rina a kaba inji CITES
2016-01-12 10:16:17 cri

Taron dandalin masu ruwa da tsaki game da yaki da cinikayyar sassan dabbobin daji dake fuskantar barazana ko CITES a takaice, ya fidda wasu alkaluma dake nuna cewa daga shekarar 2011 ya zuwa yanzu, an samu raguwar yawan giwayen dake hallaka a nahiyar Afirka, a sakamakon farautar su da ake yi ba bisa ka'ida ba.

Mahalarta taron na CITES wanda ya gudana a jiya Litinin a birnin Geneva, sun ce duk da raguwar farautar giwayen, adadin wadanda ake hallakawa domin safarar hauren su na da yawan gaske.

Cikin muhimman batutuwa da taron na wannan karo ya nazarta, hadda batun hallaka giwaye da bauna domin sayar da hauren su, da kuma batun haramcin cinikayyar nau'o'in damisar yankin Asiya da dabbar pangolins, tare da hada-hadar itacen Timber mai daraja ba bisa ka'ida ba.

Kaza lika taron na duba yiwuwar dorawa wasu kasashen 7 takunkumin cinikayyar wasu nau'o'in abubuwa, bisa gazawar kasashen wajen samar da dokokin da za su bada damar aiwatar da manufofin dandalin na CITES.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China