in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika za su dauki matakan baiwa giwaye kariya
2015-11-06 10:12:19 cri

Wakilan hukumar kula da naman daji daga kasashen Afrika 20 sun gudanar da wani taro a Cotonou, babban birnin jamhuriyar Benin a ranar Laraba, inda suka amince da daukar matakan da suka dace domin kare lafiyar giwaye a nahiyar Afrika.

Wakilan sun tabbatar da hakan ne a takardar jawabin bayan taro, kuma sun cimma matsaya cewar, za'a tabbatar da kare lafiyar giwaye a fadin nahiyar, tare da daukar matakan da za su lura da rayuwar giwayen.

A yayin taron, sun gabatar da wani kuduri na neman a sanya batun cikin dokokin kasashen wajen haramta yin safarar hauren giwa a matakan cikin gida, da ma kasashen ketare.

Jami'an kula da gandun dajin daga kasashen yammaci, da gabashi da kuma tsakiyar Afrika ne suka gudanar da taron, kuma sun yi kira ga hukumomin kasashensu da na sauran kasashen duniya da ma kungiyoyin da ba na gwamnati ba na kasa da kasa, da su samar da kudaden da za'a aiwatar da shirin kare lafiyar giwayen a Afrika.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, shugaban hukumar kula da lafiyar giwaye na Afrika Patrick Omondi, 'dan kasar Kenya, ya ce, bata gari ne ke yiwa giwaye kisan kare dangi, da kuma yin safarar hauren giwar a kasashen waje, kuma lamarin na haifar da koma baya da yin karan tsaye ga doka da samar da rashin tsaro.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China