MDD ta ce, tana kokarin amincewa da wani kwarya-kwaryar taimako domin goyon bayan kokarin da Najeriya ke yi na yaki da ta'addanci a kasarta.
Wakilin babban sakataren MDD na musamman a kan harkokin yammacin Afrika Mr. Said Djinnit, ya bayyana hakan a yayin bayaninsa na bude zaman taron koli na 45 na kwanaki 2 na hukumar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika.
Djinnit, ya ce, goyon bayan MDD ga Najeriya ya biyo bayan amannar da majalisar ta yi cewar, za'a iya amfani da hanyoyi dabam-dabam, na kawo karshen rikicin da ya addabi kasar ta Najeriya.
Mr. Said Djinnit ya jaddada cewar, MDD ta damu kwarai a game da rashin tsaron da ake ci gaba da fama da shi a arewa maso gabashin Najeriya, saboda hare-haren kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram, da kuma tashin hankalin dake shafar fararen hula, wanda ke haifar da keta hakkokin jama'a, tare da haddasa babbar matsala ta sanya jama'a cikin wani hali na neman taimakon agaji. (Suwaiba)