in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyu 23 za su goyi bayan Hama Amadou a zagaye na biyu na zaben Nijar
2016-03-01 09:17:17 cri

Jam'iyyun 'yan adawa 23 a janhuriyar Nijar, sun bayyana aniyar marawa Hama Amadou baya, a yayin zagaye na biyu na babban zaben kasar dake tafe.

Wata sanarwa da gungun jam'iyyun adawar suka fitar a birnin Yamai, ta ce jam'iyyun sun amince su aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla tun kafin zagayen farko na zaben, game da marawa duk wanda ya zo na biyu a zagayen farko na zaben baya.

Shi dai Hama Amadou ya kasance na biyu ne a zaben da ya gabata da kaso 17.7 bisa dari na daukacin kuri'un da aka kada, inda yake biye da shugaban kasar mai ci Mahamadou Issoufou, wanda ya samu kaso 48.4 bisa dari na jimillar kuri'un.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China