Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nemi a dauki matakan magance korafe-korafen jama'ar kasar, inda a cewarsa, ya zama wajibi a dauki cikakkun matakai na rubanya kokarin share wa jama'a kukansu yadda ya kamata, a kokarin kiyaye hakkokinsu da moriyar al'umma bisa doka yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)