Shugaba kasar Sin Xi Jinping ya ba da umarnin ci gaba da daukar matakai na gina tsarin ayyukan yakin soji, wadanda za su dace da halayya ta musamman ta kasar Sin.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne da sanyin safiyar Larabar nan, yayin ziyarar da ya kai cibiyar ba da umarni ta ayyukan yaki, wadda shi ne babban kwamandan askarawanta, take kuma karkashin babbar hukumar lura da ayyukan soja ta kasar Sin.
Cikin jawabin da ya gabatar, Mr. Xi ya ce, ya zama wajibi a ci gaba da aiwatar da sabbin dabarun aikin soja a irin yanayin da ake ciki, tare da mai da hankali ga fannonin karantar dabarun yaki, da tsara tafiyar da shi.
Shugaba Xi wanda kuma shi ne babban sakataren jam'iyyar Kwaminis mai mulkin kasar Sin, ya bukaci dakarun rundunar sojin kasarsa da su sauya dabaru, su kuma shigar da kirkire-kirkire, da fasahohin murkushe kalubale da aka iya fuskanta, duka dai da nufin kafa tsarin runduna mai cike da karko, da da'ar aiki, tare da cikakkiyar kwarewa ta cimma nasarar yaki a dukkanin fannoni.
Ya ce, ya dace cibiyar ta kasance mai kwarewa da zama cikin shiri, a yayin yaki da kuma a lokutan zaman lafiya.(Saminu Alhassan)