Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU dake kasar Somaliya (AMISOM) ta sanar da cewa, shugabanta, Mahamat Saleh Annadif, zai yi ban kwana da wannan tawaga a wata mai zuwa, kuma mataimakiyarsa madam Lydia Wanyoto Mutende za ta maye gurbinsa, kafin a nada wani sabon shugaban wannan tawaga.
AMISOM ba ta ba da wani karin haske ba idan wannan mataki yana da alaka da irin sauyen shugabanci da aka saba.
Mahamat Saleh Annadif zai bar tawagar a ranar 2 ga watan Yulin shekarar 2014, in ji AMISOM a cikin wata sanarwa.
Mista Annadif, 'dan asalin kasar Chadi, ya kama aiki a kungiyar AU a shekarar 2006 tare da jagorantar tawagar AU a Somaliya tun daga bakin shekarar 2012.
Bisa umurnin MDD, tawagar AMISOM na kunshe da sojojin kasashen Uganda, Burundi, Djiboutie, Habasha, Kenya da Sierra-Leone, kuma an jibge wadannan sojoji a kudanci da tsakiyar kasar Somaliya. (Maman Ada)