Martin Kobler, shugaban tawagar MDD MUNUSCO a jamhuriyar demokradiyya ta Congo DRC, ya roki jama'a da su kwantar da hankulansu, musamman bayan fadan kan iyaka da aka gwabza tsakanin sojojin Congo da na Rwanda.
Kakakin MDD Farhan Haq ya bayyana wa wani taron manema labarai cewar, Kobler na ci gaba da tuntubar hukumomin Congo da na Rwanda, a kokarin da ake yi na kashe wutar rikicin, tare da sanya Rwanda da jamhuriyar demokradiyyar Congo, a kan turba aiwatar da tsarin hadin kai, na wanzar da zaman lafiya da tsaro, da kuma ci gaba da zama makwabtan juna na gari.
Sojojin Rwanda da na Congo sun yi fada da juna a cikin kwanaki biyu, a kan iyaka a ranar Alhamis, rahotanni na cewar, tashin hankalin na barazanar rikidewa zuwa yaki da juna. (Suwaiba)