in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DRC ta tusa keyar wani babban mai laifi a kisan kiyashi zuwa Rwanda
2016-03-21 10:06:52 cri

Jamhuriyar demokradiyar Kongo DRC a ranar Lahadin nan ta tusa keyar wani babban mai laifi wanda ake zargi da hannu a kisan kiyashin kasar Rwanda, Ladislas Ntaganzwa zuwa kasar shi.

Ntaganzwa wanda kotun hukunta masu aikata manyan laifuffuka ta kasa da kasa a kan Rwanda ta kai masa kara game da laifin kisan kiyashin da aka yi a shekara ta 1994 na daga cikin mutane 9 da ake nema ruwa a jallo a kan hannun shi cikin kisan, wanda ya jawo asarar rayukan 'yan Tutsis da daidaikun 'yan Hutus 800,000.

Wanda ake zargi da laifin kisan kiyashin da ya isa filin jiragen sama na Kigali ne a jirgin MDD, yana daga cikin mutanen da suka nemi mafaka, kuma Amurka ta saka kudi dala miliyan biyar a kan kowannen su in har aka kamo shi.

Kotun shari'a ta Rwanda ta karbi Ntaganzwa, wanda aka kame shi a karshen shekarar bara a jamhuriyar demokradiya ta Kongo, kuma ana sa ran zai bayyana a kotu nan da kwanaki 10, kamar yadda masu shari'ar kasar ta Rwanda suka tabbatar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China