Jamhuriyar demokaradiyyar Congo (DRC-Congo) da kasar Rwanda sun bayyana niyyarsu ta murkushe dakarun kungiyar 'yan tawayen dake kokarin tabbatar da demokaridiyya da kwato 'yancin Rwanda (FDLR) dake gudanar da ayyukanta a gabashin DRC-Congo, a cewar wata sanarwar da aka fitar bayan wani zaman taron ministocin tsaro na kasashen biyu da ya gudana a ranakun Labara da Alhamis a birnin Kigali, hedkwatar kasar Rwanda.
Taron ya baiwa ministan tsaron Rwanda James Kabarebe da ministan tsaron Congo Aime Ngoi-Mukena, damar tattauna kalubalolin tsaro da kasashen biyu suke fuskanta, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)