in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage takunkumin da aka sanyawa wasu jiragen dakon mai a Najeriya
2015-09-11 09:15:07 cri

A jiya Alhamis ne mahukuntan kamfanin sarrafa albarkatun mai a Najeriya, suka bayyana dage takunkumin da aka kakabawa wasu jiragen ruwa na dakon mai da iskar gas su 113.

Wata sanarwa da kakakin kamfanin na NNPC Ohi Alegbe ya rabawa manema labarai, ta nuna cewa, daukar wannan mataki na baiwa jiragen ruwan damar ci gaba da ayyukan su, ya biyo bayan tantance su da aka yi.

Ya ce, an dage katunkumin ne, bayan da kamfanonin suka samu amincewa daga daukacin sassan masu ruwa da tsaki a fannin dakon mai da iskar gas.

Alegbe ya kara da cewa, yanzu haka gwamnatin Najeriyar ta amince da kafa wani kwamiti na musamman, wanda zai kunshi wakilan hukumomin gwamnati daban daban, da nufin sake nazartar ayyukan jiragen dakon mai a kasar. Kaza lika ana sa ran kwamitin zai baiwa gwamnati shawarwari game da matakan da suka dace a dauka a wannan fanni domin kaucewa matsalolin da aka fuskanta a baya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China