in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da taron muhawara kan mashigin tekun Guinea ne domin mai da martani ga harkokin dake jawo hankulan kasashen Afirka
2016-04-06 19:57:18 cri
Kasar Sin ita ke rikon ragamar kwamitin sulhun MDD a wannan wata na Afrilu, a kuwa cikin watan ne za a gudanar da tarukan muhawara guda uku, ciki har da taron muhawara kan batun 'yan fashin teku a mashigin tekun Guinea.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin Lu Kang, ya bayyana cewa, za a gudanar da wannan taro ne na muhawara, domin daukar matakai na warware wasu matsaloli masu jawo hankalun kasashen Afirka, da zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.

A gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin wajen Sin ta shirya a jiya Talata, Mr. Lu Kang ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, batun 'yan fashin teku a mashigin tekun Guinea ya kara tsananta, wanda hakan ke barazana ga zirga zirgar jiragen ruwa, da tsaron tattalin arziki a wannan yanki, a sabili da haka ne kuma kasashen Afirka ke fatan yaki da wannan matsala, da samun goyon baya daga kasashen duniya.

Lu Kang ya bayyana cewa, taron zai sa kaimi ga kasashen duniya wajen samar da taimakon su, a aikin ba da kariya ga mashigin teku na Guinea ta hanyar kara karfin kasashen yankin a fannin tsaro.

Ya ce Sin na fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya, da nuna goyon baya ga kasashen dake wannan yanki, wajen yaki da 'yan fashin teku. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China