160412-tattaunawa-da-gwamnan-Kaduna-saminu-amina.m4a
|
Bisa goron gayyatar da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping ya ba shi, shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya fara ziyarar aiki a kasar ta Sin a jiya Litinin. Wakilin sashen Hausa na CRI Saminu Alhassan a jiya ya samu damar tattaunawa da gwamnan jihar Kaduna mai girma Nasir Ahmad El-Rufai, wanda ke cikin tawagar da ke wa shugaban rakiya a wannan ziyararsa, inda gwamnan ya bayyana burin da ake neman cimmawa a wannan ziyara.