Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da kungiyar tarayya kasashen Afrika AU sun yi kira da a fadada kafar samar da alluran rigakafi saboda a cikin kowane yara biyar an gano cewar guda ba ya samun dukkannin alluran da za su ceci ran shi a nahiyar Afrika.
Wannan kididdiga dai an fitar da ita ne a ranar Talatan nan cikin rahoton da ofishin yankin na WHO a Afrika da gabashin Mediterranean ta wallafa a taron farko na ministoci a kan alluran rigakafi a Afrika da ake yi tsakanin Laraban nan 24 zuwa Alhamis 25 ga wata, a cibiyar kungiyar AU a birnin addis Ababa na kasar Habasha.
A cikin shirin alluran rigakafin a nahiyar, ana da kashi 80 cikin dari wanda shi ne mafi kakanta a kowane yanki na duniya baki daya kamar yadda rahoton ya yi bayani.
Ana sa ran taron ministocin ya hada dukkan ministocin kiwon lafiya da sauran ministoci dake kan turba daya da kuma 'yan majalissun dokoki wajen ba da tabbacin su na samar da kafar samun alluran rigakafin ga jama'ar su tare da karfafa ayyukan isar da alluarn rigakafin inda ya kamata.
Daraktan yankin na ofishin WHO a Afrika Matshidiso Moeti, ya ce, in har Afrika na son cimma burin ta da kuma samun makoma mai haske, dole a hada hannu a tabbatar kowane yaro a nahiyar ya samu alluran rigakafin.(Fatimah)