Hukumar lafiya ta duniya wato WHO tare da mataimakanta ta ce, sun samar da cibiyoyin kula da lafiya ga dubban 'yan gudun hijira wadanda rikici ya raba su da matsugunansu a arewa maso gabashin Sudan ta Kudu.
A watan Fabrairun shekarar 2014 ne hukumar ta WHO ta ayyana irin mummunan yanayin da fannin kiwon lafiya ya shiga a Sudan ta Kudu, ta ce, yanayin kiwon lafiyar ya kai mataki na kuma shi ne mataki mafi girma dake bukatar daukin gagagawa.
Hukumar lafiya ta duniyar ta ce, a watan Augusta, a kalla mutane dubu 10 ne suka isa yankin Malakal, yankin dake zama garkuwa ga fararen hula bayan suka shafe tsawon wata guda suna kokarin kutsawa yankin, a yanzu haka yawan 'yan gudun hijirar dake zaune a yankin tare da iyalansu ya kai dubu 46 da 567, wadanda suke cikin mawuyacin hali na kamfar ruwan sha da rashin tsabtar muhalli.
A cewar babban jami'in sashen dake kula da barkewar cutuka a Sudan ta Kudu, Allan Mpairwe, yanzu haka yankin na Malakal ya zama matattarar dubban 'yan gudun hijirar al'ummar Sudan ta Kudu wadanda a kullum yawansu na karuwa, lamarin da ya haddasa gurbacewar ruwan sha da kuma yaduwar cutuka kamar su cutar gudawa da dangoginta da cutar hanta da dai sauransu. (Ahmad Fagam)