in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta tura jirage masu sarrafa kansu 500 domin sanya ido kan gine- ginen man fetur
2015-06-24 10:40:39 cri

Gwamnatin Najeriya ta kammala tsare-tsarenta na tura jigaren sama masu tuka kansu kimanin 500 da wasu jiragen sama domin tabbatar da sanya ido da ba da kulawa yadda ya kamata kan gine-ginen man fetur na kasar, in ji wani jami'in gwamnatin kasar a ranar Talata.

Ade Abolurin, kwamanda janar na jami'an tsaron kasar Najeriya (NSCDC) ya yi wannan sanarwa a Abuja, babban birnin kasar, bisa tsarin karfafa kokarin wannan shirin aiki.

Wasu jiragen masu sarrafa kansu, tuni an tura su a wani shiri na gwaji a wasu yankunan jihar Niger-Delta, kamar yankin Bayelsa, domin gwajin ingancin wannan mataki, in ji jami'in.

Wannan shirin na cikin tsarin niyyar da sabbin hukumomin kasar ke nunawa na warware matsalar satar mai, da kuma kara ribar da kasar ke samu daga man fetur.

Mista Abolurin ya yi allawadai da ayyukan sacen mai a cikin kasar, tare da bayyana cewa, rundunarsa tana aiki dare da rana domin kawar da wadannan munanan ayyuka.

Jami'an tsaron kasar na binciken wasu hanyoyin sanya ido kan bututun mai, musammun ma ta hanyar amfani da fasahohin zamani, da wasu kayayyakin zamani domin bin masu aikata wadannan ayyuka, in ji mista Abolurin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China