Shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang sun buga waya ga shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain, da firaministan kasar Muhammad Nawaz Sharif, domin jajantawa game da harin ta'addanci da ya auku a kasar.
Shugaba Xi Jinping da firaminista Li Keqiang, sun gabatar da sakon juyayi game da mutanen da suka mutu a sakamakon harin, kana sun bayyana ta'aziyyar su ga iyalan mamatan. Ban da haka kuma sun bayyana cewa, kasar Sin na adawa da dukkanin wani nau'i na ta'adanci. Don haka suka yi Allah wadai da aukuwar harin na baya bayan nan.
Shugabannin na Sin sun kuma ce suna goyon bayan Pakistan a fannin yaki da kasar ke yi da ta'addanci, da kuma kokarin wanzar da zaman lafiya da kuma kare rayukan jama'a. (Lami)