Jakadan kasar Sin Fu Cong, a Litinin din da ta gabata, ya bukaci a ba da muhimmanci sosai game da 'yancin bil adam dangane da batun ta'ammali da miyagun kwayoyi, inda ya tabo batu game da alfanun dake tattare da ofishin MDD mai yaki da fataucin haramtattun kwayoyi, wanda ke Vienna.
Fu, ya fada hakan ne a yayin taron mahawara na kwamitin kare hakkin bil adam na MDD karo na 31, wanda ya kunshi mambobin kasashe 28.
Fu, wanda shi ne mataimakin babban jagoran tawagar kasar Sin a MDD a taron na Geneva, ya bukaci kasashen duniya da su mutunta yarjejeniyoyin MDD uku na shekarun 1961, da 1971, da 1988, da kuma sanarwar siyasa ta shekarar 2009.
Domin samun nasarar shawo kan matsalolin dake addabar al'ummomin kasashen duniya, Fu, ya bukaci a samar da cikakken tsari wanda zai dace da yanayin tunkarar al'amuran da aka sa a gaba, sannan ya bukaci kasashen duniya da su mutunta martaba da manufofin ko wace kasa.
Wakilin na Sin, ya bukaci kasashen duniya da su hada gwiwa a tsakanin su wajen mutunta dokokin kasa da kasa.(Ahmad Fagam)