A yayin ganawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, ta'ammali da miyagun kwayoyi yana shafar tsaron kasa, da makomar al'ummar kasa da kuma albarkar jama'a. Sabo da haka, daukar kwararan matakan yakar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi mataki ne da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar Sin suke dauka a kullum. Dole ne hukumomi na yankuna daban daban na kasar su sa aikin yakar laifin miyagun kwayoyi tamkar wani nauyin siyasa da aka dora musu. Kuma ya kamata a ilmantar da jama'a, musamman yara da matasa game da yakar batun ta'ammali da miyagun kwayoyi. (Sanusi Chen)