in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya na karfafa tsaro a filin jirgin sama domin yaki da fataucin miyagun kwayoyi
2014-04-25 10:00:46 cri

Shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete ya ba da umurni a ranar Alhamis ga hukumomin da abin ya shafa da su mai da hankali, ta yadda filayen jiragen saman kasar ba za su cigaba da zama wani dandalin fataucin miyagun kwayoyi ba. A lokacin da yake aza tubulin farko na gina tashar filin jirgin saman ta uku, da aikin ginawar zai lakume kudin Euro miliyan 235 a nan babban filin jiragen saman kasa da kasa na Julius Nyerere (JNIA), dake Dar es salaam, babban birnin tattalin arzikin kasar. Mista Kikwete ya bayyana cewa, bai gamsu ba kan halin yanzu da yadda ake sanya ido da binciken miyagun kwayoyi a filayen jiragen saman kasar Tanzaniya. Musamman ma shugaban kasar ya ba da umurni ga ofishin ministan sufuri da na hukumar dake kula da filayen jiragen sama da su mai da hankali, ta yadda filin jiragen saman JNIA da filin jiragen saman kasa da kasa na Kilimandjaro dake arewacin kasar sun daina zama wuraren da ake amfani da su wajen ficewa da miyagun kwayoyi zuwa kasashen waje. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China