in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Falasdinu za ta shiga ICC, in ji babban magatakardar MDD
2015-01-08 10:48:33 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya amince da bukatar Falasdinawa ta shiga jerin kasashen dake cikin kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.

Wata kafa ta MDD ta bayyana cewa, Falasdinun za ta shiga ICC a hukunce, tun daga 1 ga watan Afirilu mai zuwa. Wannan dai matakin zai baiwa Falasdinun damar gabatar da korafinta game da Isra'ila gaban kotun ta ICC.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai wakili mai sa ido na Falasdinu a MDD Riyad Mansour, ya gabatar da takardun shiga yarjejeniyoyin kasa da kasa 16 ga MDDr, ciki hadda ta shiga kasashen dake kotun ta ICC.

Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa, tuni babban magatakardar MDDr ya tabbatar da bin ka'idojin karbar takardun, ya kuma bayyanawa dukkanin masu ruwa da tsaki hakan, bisa tanajin dokokin majalissar.

Kafin hakan, a ranar Laraba shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya rattaba hannu kan kudurin neman shiga 'yarjejeniyoyin kasa da kasa 20, bayan da MDD ta yi fatali da bukatar dakatar da Isra'ila, daga ci gaba da mamayar yankuna Falasdinawa.

A wani ci gaban kuma mahukuntan Falasdunun sun bukaci kotun ICC, da ta binciki zargin ayyukan yaki da dakarun Isra'ila suka aikata, cikin kwanaki 50 da ta shafe ta kaiwa yankin Gaza hare-hare, a watannin Yuli da Agustan shekarar da ta gabata. Matakin da ya haifar da kisan kusan Falasdinawa 2,200, da suka hada da yara kanana 400. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China