Wata kotu a Libya ta ci gaba da sauraron shari'ar jami'an tsohuwar gwamnatin shugaba Gaddafi, duk kuwa da bukatar da kotun hukunta manyan laifukan yaki ta kasa da kasa ICC ta gabatar, game da mika 'dan tsohon shugaba Gaddafi wato Saif Gaddafi zuwa birnin Hague.
Bayan dai zaman kotun na jiya Lahadi wanda bai kai ga cimma wata nasara ba, an dage zaman sauraron shari'ar zuwa ranar 22 ga watan Yuni mai zuwa.
An dai gudanar da zaman ne a gidan yarin Al-Hadba dake birnin Tripoli, inda aka tuhumi jami'an, ciki hadda tsohon babban jami'in tsaron farin kaya Abdullah Senussi, da tsohon firaministan kasar Baghdadi Mahmoudi, da laifukan da suka hada da shirya aikata fyade, da tunzura jama'a, da raba kan 'yan kasa, yayin tarzomar da ta kai ga kifar da tsohuwar gwamnatin a shekarar 2011 da ta gabata.
Kamar dai yadda ta wakana a baya, a wannan karo ma Saif Gaddafi ya bayyana gaban kotun ne ta kafar bidiyo, daga kurkukun Zintan inda ake tsare da shi.
Tuni dai kotun ICC ta bukaci a mika mata Saif Gaddafi, domin ya amsa tuhumar aikata laifukan yaki, da na keta hakkokin bil'adama, yayin waccan tarzoma ta shekarar 2011. (Saminu)