Rahotanni daga Nairobin kasar Kenya sun tabbatar da cewa, sojojin gwamnati dake aiki karkashin rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a Somaliya AMISOM sun yi nasarar hallaka 'yan mayakan Al-Shabaab 13 a wata arangama da suka yi a kudancin Somaliyan a safiyar Lahadin da ta gabata.
Kakakin rundunar tsaron kasar ta Kenya KDF Kanar David Obonyo ya ce, sojojin sun yi arangamar ne a Sarira dake mahadar Lecta kusan kilomita 30 arewa da Ras Kamboni a kudancin Somaliya.
Kanar Obonyo ya ce, sojojin gwamnatin ba su yi asarar kowa daga cikin su ba a fadan baya bayan nan wanda aka kame wani kwamandan kungiyar ta Al-Shabaab a yanzu haka ana tsare da shi.
Ya yi bayanin cewa, sojojin sun samun bin sahun 'yan kungiyar ne sakamakon bayanan sirri da suka samu na shirin kai hari, kuma a dalilin hakan aka samu kama wani kwamandan kungiyar, aka hallaka magoyan shi 13, sannan aka samu manyan bindigogi na AK 47 guda 8, bindigogin PKM masu sarrafa kan su, gurnetin harba roka 2, da kuma nau'in albarusai da dama, in ji wata sanarwar da ya fitar.(Fatimah)