Gwamnatin kasar Kenya ta sha alwashin cewa, ba za ta janye sojojinta daga kasar Somaliya ba kamar yadda 'yan ta'addan kasar suka bukata.
Mataimakin shugaban kasar Willian Ruto da yake bayanin a ranar Lahadin nan, ya ce, a maimakon hakan rundunar sojin kasar ta Kenyan na kira ga al'ummar kasar da su hada kai wajen yaki da ta'addanci a duk duniya. Ya ce, ba za'a amince ko da inci daya ne na kasar ba 'yan ta'adda su kwace.
Mr. Ruto ya bukaci 'yan Kenya da kada su amince da dabi'an dora laifin a kan abin da ya shafi tsaro, amma su yi iyakacin kokarinsu wajen yaki da ta'addanci.
Ya ce, batun tsaro yana bukatar goyon baya da kuma gudunmuwa daga daukacin al'umma idan har ana son yin nasara wajen yaki da ta'addanci. Ya kara da cewa, gwamnati tana iyakacin kokarinta wajen ganin an samar wa jami'an 'yan sanda isassun kayan aiki, musamman motoci da sauran muhimman kayayyaki.
Sannan mataimakin shugaban kasar na Kenya, William Ruto sai ya tabbatar da cewa, gwamnati za ta dauki karin jami'an tsaro 10,000 a ranar 20 ga watan nan da muke ciki domin su fara daukan horo cikin sauri. (Fatimah)