Sabon zababben shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR Faustin Archange Touadera, ya yi alkawari karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a matsayin babbar aminiyar ga kasar.
Touadera, ya fadi hakan ne a yayin zantawa da kamfanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce, CAR tana bukatar yin aiki tare da kasar Sin, domin kulla abokantaka da karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu.
Touadera ya ce, akwai matukar bukatar farfado da ci gaban kasar cikin gaggawa, bayan shafe shekaru uku tana fuskantar yakin basasa, ya kara da cewar, sabuwar gwamnatin kasar, za ta ba da fifito ne wajen samar da tsaro, da zaman lafiya, da samun maslaha, da kuma hana yaduwar makamai a tsakanin jama'a.
Touadera ya jaddada muhimmancin farfado da tattalin arzikin kasar, yana mai cewa, CAR tana bukatar taimakon kasashen duniya domin dawo da yanayin tattalin arzikin kasar cikin hayyacinsa.(Ahmad Fagam)