in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a CAR
2016-02-14 09:35:04 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon a ranar Asabar da ta gabata ya bukaci al'ummar jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR, ciki har da 'yan takara a zabukan kasar, da su tabbatar an gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da na majalisun dokokin kasar wadanda ake sa ran gudanarwa a ranar Lahadin nan.

A sanarwar da mai magana da yawun babban sakataren ya fitar, ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki a kasar da su tabbatar da an gudanar da zabukan cikin lumana kamar yadda ke kunshe cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin 'yan takarar da jam'iyyun siyasar kasar.

Ban, ya bukaci bangarorin dake kalubalantar juna da su warware duk wata takaddama ta hanyar matakan shari'a, sannan ya gargadi duk wasu masu yunkurin tada zaune tsayi a kasar.

Ana sa ran masu kada kuri'a a CAR za su gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a Lahadin.

Babu wanda a cikim 'yan takarar shugabancin kasar 30 ne ya samu kuri'un kashi 50 cikin 100 a zagayen farko na zaben, wanda aka gudanar a ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2015 da ta gabata.

Ana sa ran zaben zai kawo karshen rikicin da ya jima yana addabar jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China