in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanya takunkumi ga mayakan LRA na CAR
2016-03-09 10:01:17 cri

Sashen adana kudade na Amurka ya sanar da sanya takunkumi ga kungiyar mayakan 'yan tawaye na jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR wato LRA a takaice, da kuma shugabanta Joseph Kony.

Wata sanarwar da sashen adana kudaden na Amurka ya fitar, ta sanar da cewar, Amurka ta rufe asusun ajiyar kudaden na LRA dake karkashin ikonta, sannan ta haramta duk wata mu'amalar kudade tsakaninta da kungiyar.

Ita dai kungiyar LRA, wadda Joseph Kony ke jagorantar ta, ta yi kaurin suna wajen aikata kisan kiyashi, da cin zarafin fararen hula, da kuma yin garkuwa da kananan yara domin tilasta su shiga aikin soji, ko kuma bautar da su.

Mai rikon mukamin daraktan ofishin kula da kaddarori na kasashen waje John E. Smith, ya fada cewar, baya ga hallaka fararen hula da ba su ji ba su gani ba, har ila yau kungiyar ta LRA tana haddasa yawan tashe tashen hankula.

Smith ya ce, wannan matakin da sashen tsumi na Amurkar ya dauka, zai taimaka wajen dakile ayyuykan kungiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China