in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu ta karyata rahotannin sauyin majalisar zartarwarta
2016-03-21 09:23:56 cri

Fadar shugaban kasa a Afrika ta kudu ta karya rade radin dake cewa, shugaba Jacob Zuma zai yi wa majalisar zartarwar shi gyaran fuska a wannan makon da aka shiga.

A cikin sanarwar da kakakin fadar shugaban kasar Bogani Majola ya fitar a ranar Lahadin nan, ya ce, rahoton da wata jaridar Independent ta kasar ta fitar ba gaskiya ba ne, yana mai bayanin cewa, a cikin rahoton, an ce wai shugaba Zuma yana shirin cire minista a fadar shugaban kasa Jeff Radebe da ministan ci gaban tattalin arziki Ebrahim Patel, ministan ciniki da masana'antu Rob Davies, da kuma ministan ilimi da horaswa Blade Nzimande.

Rahoton makarkashiya ce wadda a bayyane take nuna kudurin kawo baraka, kokwanto da kuma rudani, in ji Mr Majola.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China