Rundunar tsaron Afrika ta kudu ta yi watsi da rade radin da ake bazawa, cewar, za ta aike da dakarunta zuwa Najeriya domin yaki da kungiyar Boko Haram.
Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Afrika ta kudu Siphiwe Dhlamini, ya fada wa manema labarai cewar, kawo yanzu gwamnatin kasar ba ta zartar da wani kuduri ba na tura dakarunta don yakar kungiyar Boko Haram.
Jita jitar dai ta kunnu kai ne, tun lokacin da shugaba Jacob Zuma na Afrika ta kudun ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa Najeriya a wannan mako, domin tattaunawa game da tura dakarun tsaro na musamman don ci gaba da yakar kungiyar mai kaifin kishin Islama.
Wannan rade radin ya ci gaba da bazuwa ne, bayan da ministan tsaron Afrika ta kudu Nosiviwe Mapisa-Nqakula ya gana da takwaransa na Najeriyar Mansur Dan Ali a farkon wannan makon.
A sanarwar da aka fitar bayan tattaunawar su da shugaba Muhammad Buhari, Zuma ya bayyana cewar, ganawar tasu ta tabo batun yin hadin gwiwa a matakin shiyya, da ma nahiyar domin dakile ayyukan ta'addanci.(Ahmad Fagam)