Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ya bayyana aniyar kasar sa ta gudanar da gwajin makaman Nukiliya, tare da makamai masu linzami kirar roka nan da dan lokaci mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran kasar KCNA ne ya rawaito shugaba Kim na bayyana hakan, yayin da yake duba aikin gwaji na tsara muhallin harba makami mai linzami na kasar.
An gudanar da aikin gwajin ne domin tantance sabbin fasahohin da kasar za ta yi amfani da su a nan gaba, domin tabbatar da nasarar harba makamai masu linzami.
KCNA ya ce, an cimma nasara a gwajin sabbin fasahohin da kasar ta aiwatar.(Saminu)