in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DPRK ta yi kira da a dakatar da arangama tsakaninta da Korea ta Kudu
2014-07-07 10:36:36 cri

Gwamnatin Korea ta Arewa DPRK ta yi kira da a kawo karshen arangama tsakaninta da Korea ta Kudu, tare da kara dankon dangantaka tsakaninsu.

Wannan kiran na kunshe a cikin wata sanarwar gwamnati, wacce aka baiwa kamfanin dillancin labarai na kasar KCNA.

Korea ta Arewa ta gabatar da wadansu shawarwari guda hudu, wadanda suka fayyace manufofinta da alkiblar da ta dauka wajen dakusar da tashin hankali a tsibirin na Korea, tare da kaiwa ga nasarar hadewar arewaci da kudancin tsibirin, wato shekaru 20 bayan rasuwar tsohon jagoran kasar, Kim II Sung. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China