in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana hasashen tattalin arzikin Zimbabwe zai bunkasa a shekarar 2016
2015-11-27 09:46:49 cri

Ministan harkokin kudi na kasar Zimbabwe Patrick Chinamasa ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasarsa zai bunkasa daga kashi 1.5 cikin 100 a wannan shekara zuwa kashi 2.7 cikin 100 a shekarar 2016.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2016 na dala biliyan 4 a majalisar dokokin kasar. Ya ce, ana sa ran bunkasar dukkan bangarorin tattalin arzikin kasar da a kalla kashi 1.3 cikin 100 zuwa kashi 4.5 cikin 100 a shekara mai zuwa.

Ministan ya ce, kasasfin kudin kasar zai mayar da hankali ne ga matakan farfado da tattalin arziki, da samar da yanayin da ya dace ga masu sha'awar zuba jari daga ketare.

Mr Chinamasa ya kara da cewa, hasashen ci gaban kasar ya dogara ne ga irin matakan da aka tsara na warware bashin dala biliyan 1.8 da kasar ta ciwo a farkon rabin shekara mai kamawa, ta yadda za a samu damar karbo sabon rancen da zai taimaka wajen farfado da tattalin arzkin kasar da ya durkushe.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China