Gwamnatin Najeriya tana shirin kara azama domin kara karfin matatun danyen manta na cikin gida a shekarar 2015.
Mai da hankalin kan matatun man na cikin gida zai iyar kawo karshen matsalolin da suka shafi bangarorin man da gas na kasar, in ji Bayo Olowoshile, sakatare janar na kungiyar masanan mai da gas ta Najeriya, a lokacin da yake hira tare da manema labarai a ranar Litinin a birnin Lagos.
A cewarsa, matakin farko na gwamnatin Najeriya a shekarar 2015, zai shafi ba da kwarin gwiwa ga matutun man na gida, nau'o'in mai kamar kanarzil, man fetur da sauransu da kuma kayayyakin da suka jibanci man fetur.
Aikin cikin gida na sarrafa gas domin makamashi, masana'antu, noma da motoci ya kamata ya samu kulawa sosai a wannan sabuwar shekara, in ji sakatare janar din wannan kungiya.
A nasa ra'ayi, ya kamata gwamnatin Najeriya ta rage adadin shigo da kayayyakin man fetur da kashi 50 cikin 100, tare da kara cewa, kafa ayyukan yi da amfani da karfin aiki zai kasance abun mai da hankali ga gwamnati a cikin yanayin da ake ciki na karuwar tashe tashen hankali da kashe kashe.
Yawancin matatun man fetur na Najeriya ba sa aiki dukkansu, lamarin da ya tilastawa kasar dake yammacin nahiyar Afrika shigo da yawancin man fetur da na man diesel da take sha. (Maman Ada)