Gwamnatin Najeriya ta karyata zargin da ake cewa, tana shirin sake fasalin kasafin kudin da ta yi na shekara 2015 kan farashin mai.
Wannan batu na kunshe cikin wata sanarwa da ministar kudin kasar Ngozi Okonjo-Iweala ta fitar jiya ta hannun kakakinta Paul Nwabuikwu.
Sanarwar ta ce, har yanzu Najeriya ba ta yi shiri na sake fasalin kasafin kidinta ba bisa farashin man, duk da cewa har yanzu farashin man bai tashi ba a kasuwannin duniya.
A cewarsa, akwai matakai da dama da za a dauka sakamakon faduwar farashin man. Sannan suna hada kai da 'yan majalisun kasar don daukar hanyoyin da za su kai kasar ci gaba a wannan lokaci.
A watan da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta shirya rage kasafin kudin na wannan shekara da kashi 8 cikin 100, sannan ta rage farashin man zuwa dala 65 kan ko wace ganga maimakon farashin shekarar da ta gabata na dala 77 da Centi 50 kan ko wace ganga, sakamakon faduwar farashin man a kasuwannin duniya.
Tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ce, farashin man ya yi faduwar da ba a taba ganin irinsa ba a kasuwannin duniya, lamarin da ya hargitsa kasuwannin kasar, kudaden ajiyarta na ketara, sannan ya tilastawa masu tsara manufofi rage darajar kudin kasar wato Naira a karon farko cikin shekaru 3.
Najeriya dai na samun kashi 70 cikin 100 na kudaden shigarta ne daga fitar da danyen mai, kuma hakan na iya tilastawa hukumomin kasar zaftare kudaden da za su kashe a zaben wannan shekara. (Ibrahim)