Babban mashawarci a majalissar zartaswar kasar Afirka ta Kudu Jeff Radebe, ya ce, har ya zuwa yanzu akwai kyakkyawar alaka tsakanin kasarsa da Najeriya, duk kuwa da tara ta dalar Amurka biliyan 5.2, da mahukuntan Najeriyar suka dorawa kamfanin sadarwa na MTN na kasar Afirka ta Kudun.
Mr. Radebe wanda ya bayyana hakan ga wani taron manema labarai a jiya Alhamis, bayan kammalar taron majalissar zartaswar kasar, ya ce, batun tarar da aka ci kamfanin na MTN batu ne na dokokin kasawancin Najeriya. Ya ce, yana fata alakar dake tsakanin Afirka ta Kudu da Najeriya za ta ci gaba da bunkasa kamar yadda ya kamata.
Mahukuntan Najeriyar sun ci tarar kamfanin sadarwa na MTN ne, sakamakon kin bin dokar rufe layukan wayar sa marasa rajista da yawan su ya kai miliyan 5.1, wanda hakan ya ba da dama ga wasu bata gari, suka yi amfani da layukan kamfanin wajen neman kudin fansa, bayan sun yi garkuwa da tsohon ministan kudin kasar Olu Falae.
Tarar da aka dorawa kamfanin na MTN ta sabbaba dakatar da cinikayyar hannayen jarin kamfanin a ranar Litinin din da ta gabata, kafin daga baya a ci gaba da hada-hadar su, bayan da kamfanin ya bayyana cewa, yana tattaunawa game da matsalar da ya fada, tare da hukumomin da lamarin ya shafa.(Saminu)