in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta karkare taronta a babban birnin Habasha
2016-02-01 10:12:51 cri

An kammala taron koli na kungiyar hadakan kasashen Afrika AU karo na 26 mai taken "2016, shekarar hakkin bil adama ta Afrika, musamman 'yancin mata".

An gudanar da taron shugabannin kasashen mambobin na AU karo 26 ne tsakanin ranakun 30 zuwa 31 ga watan Janairu a helkwatar hukumar dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

A jawabinsa na rufe taron, sabon zababben shugaban kungiyar, shugaba Idriss Déby Itno na kasar Chadi, ya tabo muhimman batutuwan da suka shafi yadda za'a hada gwiwa wajen warware rikice rikice da ake fama da su a kasashen Afrika, da kuma batun matsalar 'yan gudun hijira.

Déby ya ce, AU na da gagarumin aiki a gabanta wajen daukar dukkannin matakan da za su magance kalubalen dake damun nahiyar.

Ya ce, kungiyar AU tana sahun gaba wajen tunkara da kuma dakile duk watar tashe tashen hankula da ta addabi kasashen na Afrika, da kuma daukar matakan samar da zaman lafiya da bunkasar ci gaba, da biyan muradun al'ummomin kasashen.

Déby, ya ce, zai yi iyakar kokarinsa don ganin an cimma muradun da aka sanya gaba a cikin wa'adin aikin sa na shekara guda.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China