Shugabar hukumar zartaswar kungiyar AU uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta bayyana matukar godiya, ga daukacin wadanda suka taimaka a yakin da aka sha da cutar Ebola a yammacin Afirka.
Zuma ta bayyana hakan ne a jiya Lahadi, a jawabin ta na kammala taron yini biyu, karo na 26 da kungiyar ta AU ta gudanar a kasar Habasha. Ta ce, dole ne a jinjinawa sassa daban daban, da suka tallafawa kungiyar AU wajen shawo kan wannan annoba da ta addabi bil Adama.
Nkosazana Dlamini-Zuma, ta godewa kasashen Afirka, wadanda suka aike da jami'an ba da agaji 855 zuwa yankunan da cutar ta fi kamari, karkashin shirin dakile cutar da aka yiwa lakabi da ASEOWA.
Bugu da kari, Zuma ta jaddada ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su sanadiyyar wannan hidima, daga kungiyoyi masu zaman kan su da hukumomin kasashen duniya daban daban, da ma dukkanin wadanda suka ba da tasu gudummawa.(Saminu)