in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar AU ta ziyarci Burundi domin warware rikicin siyasar kasar
2016-02-26 10:09:35 cri

Babbar tawaga mai kunshe da shugabanni biyar da kungiyar hada kan kasashen Afrika AU ta tura ta isa kasar Burundi domin ganawa da mahukuntan kasar, ta yadda za a lalibo hanyoyin warware dambarwar siyasar da ta dabaibaye kasar, wacce ke gabashin Afrika tun a watan Afrilun shekarar 2015.

Tawagar mai mutane biyar, ta hada da shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, da na Mauritaniya Muhammad Ould Abdul Aziz, da shugaban Senegal Macky Sall da na Gabon Ali Bango Ondimba da kuma firaiministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn.

Ministar harkokin wajen Afrika ta kudu Maite Nkoana Mashabane, wacce tana daga cikin tawagar kasar Afrika ta kudun, ta bayyana cewar, tawagar wakilan na AU sun ziyarci Burundi ne domin aikin tabbatar da zaman lafiyar kasar.

Mashabane ta ce, dukkanin shiyyoyi biyar sun hallara a Burundi, domin tattauna yadda za'a warware takaddamar siyasar kasar, kuma tun daga lokacin da tawagar ta isa kasar sun cimma gagarumar nasara, sannan akwai kyakkyawar fatar samun nasara a yunkurin tabbatar da zaman lafiyar kasar.

A cewar ta, tawagar ta kaiwa kasar sakon zaman lafiya ne.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China