in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WFP ta dakatar da jigilar abinci da take baiwa 'yan gudun hijira na Syria saboda karancin kudi
2014-12-02 14:55:30 cri

Hukumar samar da abinci ta MDD WFP ta bayyana cewar, ta dakatar da wani muhimmin shiri da take aiwatarwa na bayar da takardar amsar abinci ga wasu 'yan gudun hijira miliyan 1.7, 'yan asalin kasar Syria, wadanda a yanzu haka suke zama a kasashen da ke makwabtaka da Syria saboda matsalar rashin kudi.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya yi gargadin cewar, daukar wannan matakin dakatar da tallafawa 'yan gudun hijirar, zai sanya jama'a cikin wani halin kaka nika yi, musamman saboda gabatowar lokacin hunturu.

Kakakin MDD ya ce, hukumar abincin ta duniya tana bukatar dalar Amurka miliyan 64 a cikin gaggawa domin taimakawa 'yan gudun hijirar na Syria a cikin wannan wata na Disamba.

A karkashin shirin 'yan gudun hijirar na Syria, wadanda ke zaune a Lebanon, Turkiyya, Iraqi, da Masar suna amfani da takardar karbar abincin wajen sayen abinci a kantunan kasashen.

Hukumar samar da abincin ta MDD ta jaddada cewar, dakatar da bayar da abincin ga 'yan gudun hijirar zai haifar da tabarbarewar lafiya da kariyar su, kuma hakan na iya haddasa fitina a kasashen da suka ba su masabki, daga nan sai ya yi kira a kan duk wadanda ke da muradin bayar da gudumuwa da su yi hobbasa a cikin gaggawa kafin a shiga cikin hali mai tsanani. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China