in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WFP ta yi maraba da sake bude kogin Nil domin jigilar taimakon abinci
2014-12-30 10:41:46 cri

Hukumar tsarin abinci ta duniya ta MDD (WFP) ta yi maraba a ranar Litinin bisa karon farko da aka isar da taimakon abinci zuwa kasar Sudan ta Kudu ta hanyar ruwan kogin Nil tun fiye da shekaru.

Wani jirgin daukon kaya da WFP ya yi amfani da shi tun daga birnin Kosti na kasar Sudan dauke da ton 450 na abinci ya isa biranen Renk da Wadakona dake gundumar Haut-Nil ta Sudan ta Kudu.

Wannan abinci zai taimaka wajen ciyar da mutane kimanin dubu 28 a tsawon wata guda, dake kuma cikin shirin aikin da aka kaddamar a cikin watan Nuwamban da ya gabata, wanda ke da manufar isar da taimakon abinci a kasar Sudan ta hanyar ratsa kasar Sudan.

Wannan ne karon farko tun yau fiye da shekaru, muka samu zarafin yin amfanin da ruwan kogin Nil domin isar da abinci ta kan iyakar dake tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, kuma muna nuna godiyarmu ga duk wadanda suka taimaka wajen sake bude wannan hanyar mai muhimmancin gaske wajen kai abinci, in ji Stephen Kearney, wakilin WFP a Sudan ta Kudu a cikin wata sanarwa.

Wannan lamari ya canja halin da ake ciki game da ci gaban kokarin da ake domin isar da taimakon abinci ga mutanen dake cikin mawuyacin hali, in ji mista Kearney. Jigilar taimakon abinci tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, an dakatar da yawancinsu tun lokacin rufe iyaka tsakanin kasashen biyu, bayan da kasar Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kanta a shekarar 2011. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China