in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za'a magance rikicin kasa da kasa ta hanyar soji ba, in ji Ban Ki-moon
2016-03-07 10:32:15 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ce, ba za'a iya warware rikicin kasa da kasa ta hanyar amfani da karfin soji ba, sai dai idan ana maganar batun yaki da ta'addanci ne.

Mista Ban ya fada a yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da ministan harkokin wajen Algeriya Ramtane Lamamra cewar, babu wani matakin soji da zai iya magance rikicin kasa da kasa, in dai ba batu ne na yaki da ta'addanci ba, Ban ya ce, ana iya warware rikicin siyasar kasa da kasa ne kadai ta hanyar tattaunawar sulhu.

Da yake buga misali da rikicin siyasar kasar Libya, Ban, ya jaddada muhimmancin tattaunawar sulhu, ya kara da cewar, wannan shi ne irin abin da kasar Aljeriya take gudanarwa a halin yanzu domin warware rikicin siyasar kasar, sannan ya ce, a shirye yake ya yi aiki da dukkanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna domin warware rikicin kasar.

Sakatare janar din, ya bukaci kasashen duniya da su hada karfi da karfe domin shawo kan rikicin siyasar da ya dabaibaye Libya, muddin ba'a warware rikicin ba, al'umma zasu ci gaba da shiga mawuyacin hali a kasar.

Lamamra ya jaddada muhimmancin amfani da tattaunawa a matsayin hanyar warware dambarwar siyasar kasar ta Libya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China