in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin a shirye take ta taimaka wa ci gaban tattalin arzikin Aljeriya
2016-01-19 10:21:03 cri

Kasar Sin ta ce, a shirye take ta taimaka wa ci gaba da kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasar Aljeriya, kamar yadda jakadan ta dake kasar Yang Guangyu ya tabbatar a a ranar Litinin din nan.

Kasar Aljeriya dai tana fama da rikicin tattalin arziki wanda ta dogara har yanzu a kan albarkatun mai.

Saukan da farashin mai ya yi warwas daga dala 110 ganga daya zuwa dala 30 ganga daya a shekara ta 2014 ya sa gwamnati ta tsuke bakin aljihu domin kauce wa mummunan rikicin kudi.

Jakadan ya tunatar da alkawarin shugaban kasar Sin Xi Jinping a lokacin taron Sin da Afrika FOCAC da aka yi a kasar Afrika ta kudu na ba da gudunmuwar kudi har dala biliyan 60 a cikin shekaru 3, domin taimaka wa ayyukan hadin gwiwwar tattalin arzikin Sin da Afrika.

Ya ce, kasar Sin ta yaba matuka bisa ga kokari da matakai da mahukuntar Aljeriya suka dauka don inganta yanayin zuba jari. Abin da ya sa ya ce, za'a yi kokari fiye da kasuwanci kawai na inganta sahihanin hadin gwiwwa na cinikin kasa da kasa.

A bangaren ciniki da kasashen waje kuwa, Sin tana matakin koli wajen samar da kudi har dala biliyan 8.2 a shekara ta 2014 daga cikin dala biliyan 58.3 na kayayyakin da aka shigar, inda ta wuce kasar Faransa sau biyu a jere.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China