Ministan masana'antu da ma'adinai na kasar Aljeriya, Abdeslam Bouchouareb ya sanar a ranar Lahadi a birnin Alger cewa, za'a gudanar da wani dandalin tattalin arziki tsakanin Aljeriya da Burtaniya a cikin watan Mayu mai zuwa a birnin Alger.
Jami'in Aljeriyan da ya karbi manzon musammun na faraministan kasar Burtaniya game da huldar tattalin arziki da kasar Aljeriya, Lord Richard Risby, ya tunatar cewa, dandali na baya ya gudana a cikin watan Disamban shekarar 2014 a birnin Landan. Ko da yake masu zuba jari 'yan kasar Burtaniya ba su da yawa a kasar Aljeriya, amma akwai masu zuba jari da suka yi suna a duniya kamar HSBC a bangaren kudi, GSK da Mazraa a bangaren kiwo domin samar da madara. (Maman Ada)