in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da harin ta'addacin IS a Iraki
2016-03-01 11:23:46 cri

Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da hare-haren ta'addancin da kungiyar IS ta kaddamar a Bagadaza da garin Muqdadiya dake gabashin kasar.

A farkon ranar Litinin din da ta gabata ne, 'yan kunar bakin wake suka kaddamar da harin a kusa da garin Muqdadiya, inda ya yi sanadiyyar hallaka mutane a kalla 34, sannan wasu 43 suka jikkata. A ranar Lahadin da ta gabata ma, mutane 53 ne aka kashe tare da raunata wasu 117 a sanadiyyar fashewar wasu tagwayen boma bomai a wata kasuwa dake birnin Bagadaza.

A wata sanarwar da mai magana da yawun sakataren MDD ya fitar, Ban ya yi tur da wadannan hare haren da ya kira a matsayin harin ne na matsorata wanda suke kaddamarwa kan jama'a a lokutan da suke gudanar da jana'iza, da kasuwanni, da wuraren ibadu domin haifar da kiyayya a tsakanin al'ummar kasar Iraki.

Iraki na fuskantar tabarbarewar zaman lafiya ne tun bayan da kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama ta kwace ikon wasu yankuna a arewaci da yammacin Iraki a watan Yunin shekarar 2014.

MDD ta ayyana cewar, mutane sama da dubu 22,300 ne aka hallaka tun bayan barkewar tashin hankali a kasar a shekarar 2015.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China