Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana takaici game da abin da ya kira gallazawa, da kiristoci ke fuskanta daga 'yan kungiyar Islamic State ISIS, a yankunan da kungiyar ta ayyana a matsayin kasar musulunci da take karewa.
Wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ta rawaito Mr. Ban na nuna damuwarsa ga rahotannin dake cewa, a birnin Mosul, ISIS din na tirsasawa kiristoci musulunta, ko biyan tara, ko ma barin gidajen su.
Babban magatakardar MDDr ya ce, duk wata muzgunawa kan fafaren hula bisa dalilai na kabilanci, ko addini, ko yankin da suka fito, laifi ne na keta hakkin dan Adam, kuma wajibi ne a hukunta masu aikata hakan.
Daga nan sai ya ja kunnen dukkanin kungiyoyi da su girmama dokokin kasa da kasa, wadanda suka jibanci kare martabar dan Adam, yana mai jaddada aniyar MDD, ta samar da tallafin jin kai ga wadanda rikicin yankunan Iraqi ya ritsa da su. (Saminu)