in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar MDD a Bagadaza ta ci karo da wani abun fashewa
2014-11-17 10:07:46 cri

Tawagar MDD a birnin Bagadaza na kasar Iraqi ta ci karo da wani abun fashewa a safiyar Lahadin nan. Babu wanda ya ji rauni ko ya rasa ransa a lokacin, in ji wata sanarwa daga ofishin ayyukan taimakon Iragi na Majalissar.

Sanarwar ta yi bayanin cewa, fashewar wani abun ya faru ne lokacin da motocin tawagar guda 3 suke taso daga filin saukan jiragen sama, za su shiga cikin gari. Dukkan ma'aikatan MDD sun isa masaukinsu lafiya kalau, sai dai daya daga cikin motocin ya lalace sosai.

A cikin sanarwar da ya fitar, wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar Iraqi, Nickolay Mladenov ya ce, wannan abin da ya faru ba zai dakushe kokarin majalissar wajen ayyukanta na taimakawa kasar ta Iraqi da al'ummarta ba, wadanda suke zaune cikin tashin hankali na lokaci mai tsawo. Don haka ya ce, yana sa ran ci gaba da aiki tare da gwamnatin Iraqi domin tabbatar da cewar, za a gurfanar da masu aikata wadannan mugayen ayyuka a gaban kuliya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China