Mataimakiyar sakatare janar na MDD kan harkokin jin kai, Valerie Amos, za ta kai wani rangadin aiki a kasar Iraki daga ranar 11 zuwa 14 ga watan Satumba domin kimanta yadda cibiyoyin ba da agaji na MDD za su iyar tallafawa hukumomin kasar Iraki wajen kai dauki ga mutanen dake cikin bukata.
A yayin ziyararta, madam Amos za ta gana da manyan jami'an kasar Iraki da na yankin Kurdawa. Haka kuma za ta kai ziyara a wani sansanin 'yan gudun hijira, in ji cibiyar dake kula da harkokin jin kai ta MDD (OCHA) a cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Laraba.
Kusan 'yan kasar Iraki miliyan 1,8 suka kaura daga muhallinsu tun farkon wannan shakara, kuma tare da yanayin sanyi dake kusantowa, cibiyoyin ba da agaji da abokan aikinsu na Iraki za su cigaba da karfafa ayyukansu, in ji cibiyar OCHA. (Maman Ada)