Hukumar kwallon kafa ta Nigeriya NFF ta gayyaci babban kocin Super Eagles Stephen Keshi domin bayyana gaban kwamitin ladabtarwarta a kan sunan shi da ya bayyana cikin masu neman aiki a kasar Kwadibuwa.
Ana dai sa ran kocin ya yi bayani game da yadda aka yi hakan ya faru na bayyanar sunan shi cikin masu neman aiki a kasar ta Kwadibuwa.
Hukumar kwallon kafar ta kasar Kwadibuwa FIF dai a ranar Jumma'a ta sanar da cewa, ta samu takardun neman aiki daga wajen mutane 59 da suka hada da Stephen Keshi, a wani yunkuri na musanya babban kocinta, 'dan Faransa Herve Renard.
Sai dai kuma shi Keshi ya ce, bai san kome ba kan batun, amma ya ce bayyanar ce a gaban kwamitin ladabtarwa na hukumar NFF ba zai hana shi gudanar da aikin shi ba, yana mai bayanin cewa, ba wani sabon abu ba ne ga ko wane da ya bayyana gaban kwamitin ladabtarwar domin karin haske a kan wassu manyan al'ammura da suka daure kai. (Fatimah)