Majiyoyin 'yan sandan sun bayyana cewa, a kalla mutane 13 ne suka mutu, kana wasu sama da 20 suka jikkata yayin da wani bam da aka dana a cikin wata mota ya fashe a garin Baidoa da ke kudancin Somaliya.
Yanzu dai an killace garin tare da takaita zirga-zirga a ciki da wajen wurin da fashewar ta faru da kuma kusa da ofisoshin gwamnati da na tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU (AMISOM).
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, sai dai kungiyar Al-Shabaab mai alaka da kungiyar Al-Qa'ida ta kan kai irin wadannan hare-hare kan ofisoshi gwamnatin da na AMISOM. (Ibrahim)